42 Teku ta malalo a kan Babila, Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta.
42 Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta.
Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.
“Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.
Gama Ubangiji yana lalatar da Babila, Yana kuma sa ta kame bakinta na alfarma, Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman ruwa, Suna ta da muryoyinsu.
Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu, Suna ta da muryarsu da ruri.
Kakan kwantar da rurin tekuna, Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa, Kakan kwantar da tarzomar jama'a.
Zurfafan tekuna suna kiran junansu, Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri! Igiyoyin ruwa na baƙin ciki Suka yi wa raina ambaliya.
Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni, Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.
Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Halaka ta auko mini a kai a kai.
Wannan shi ne jawabi a kan Babila. Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.
domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.
“'Ya'yansa maza za su tara babbar rundunar yaƙi. Ɗayansu zai mamaye kamar rigyawa, har ya kai kagara wurin da abokan gāba suke.
Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.