Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan.
Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom.