Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi.
Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama'arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa 'ya'ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha'anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba.