Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata, An sa wa wuraren zamanta wuta, An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
“Za su zama kamar budu, Wuta kuwa za ta ƙone su ƙurmus! Ba ma za su ko iya ceton kansu ba. Harshen wuta zai fi ƙarfinsu, Ba wutar da za su zauna, su ji ɗumi!
Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.