Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 51:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Duniya ta girgiza, tana makyarkyata saboda azaba, Gama nufin Ubangiji na gāba da Babila ya tabbata, Nufinsa na mai da ƙasar Babila kufai, inda ba kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 51:29
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Garuruwanta sun zama abin ƙyama, Ta zama hamada, inda ba ruwa, Ƙasar da ba mazauna, Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.


Daga Dan, an ji firjin dawakai. Dakan ƙasar ta girgiza saboda haniniyar ingarmunsu. Sun zo su cinye ƙasar duk da abin da suke cikinta, Wato da birnin da mazauna cikinsa.”


Shi ya sa ƙasar za ta girgiza, Duk wanda yake cikinta zai yi baƙin ciki. Ƙasa duka za ta girgiza. Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.


Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango.


Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta.


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljannu, Matattarar kowane baƙin aljani, Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.


Duniya takan girgiza saboda ita, Sammai sukan yi rawar jiki. Rana da wata sukan duhunta, Taurari kuwa sukan daina haskakawa.


Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.


Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu?


Akwai takobi a kan masu sihiri Don su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta Don a hallaka su.


Duniya za ta girgiza sa'ad da ta ji an ci Babila da yaƙi. Za a ji kukanta cikin sauran al'umma.”


Ba za a sami dutsen yin kusurwa, ko na kafa harsashen gini a cikinka ba, Amma za ka zama marar amfani har abada.”


Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita, Sarakunan Mediyawa, da masu mulkinsu, da shugabanninsu, Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.


Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.


Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ