Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 51:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Ku ta da tuta a duniya, Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho, Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita, Ku kirawo mulkokin Ararat, da na Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita. Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai shugabanci yaƙin da za a yi da ita, Ku kawo dawakai kamar fāra.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 “Ku tā da tuta a ƙasa! Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe! Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita. Ararat, Minni, da Ashkenaz. A naɗa shugaba gāba da ita; ku shirya dawakai kamar fāra.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 51:27
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.


'Ya'yan Gomer, maza, su ne Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.


Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat.


Ku ta da tuta don a faɗa wa garun Babila, Ku ƙarfafa matsara, Ku sa su su yi tsaro, Ku kuma sa 'yan kwanto! Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwa aikata Abin da ya faɗa a kan mazaunan Babila.


“Ku ba da labari ga sauran al'umma, ku yi shela, Ku ta da tuta, ku yi shela, Kada ku ɓuya, amma ku ce, ‘An ci Babila da yaƙi, An kunyatar da Bel, An kunyatar da siffofinta, Merodak ya rushe, Gumakanta kuma sun ragargaje!’


Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”


Ubangiji Mai Runduna ya rantse da zatinsa, ya ce, “Hakika zan cika Babila da mutane kamar fāra, Za su kuwa raira waƙar nasara a kanta.”


Kowane mutum da yake a duniya ya kasa kunne, kowannen da yake zaune a duniya, ya duba tutar, alama da za a ɗaga sama a ƙwanƙolin duwatsu, ya kasa kunne ga busar ƙaho!


Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


Zai yiwu mutane su rasa firgita, Idan aka busa ƙahon yaƙi a birni? Zai yiwu wata babbar masifa ta auko wa birni Ba da yardar Ubangiji ba?


Ni Ubangiji na ce, za su sari kurminta, Ko da yake ba su ƙirguwa, Gama suna da yawa kamar fara, Ba su lasaftuwa.


“Ya ku mutanen Biliyaminu, ku gudu neman mafaka, Daga cikin Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, Ku ba da alama a Bet-akkerem, Gama masifa da babbar halaka sun fito daga arewa.


Sa'ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.


Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.


Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran 'ya'yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.


“Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”


Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe daga arewa Su faɗa wa Babila da yaƙi. Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su cinye ta. Kibansu kamar na gwanayen mayaƙa ne Waɗanda ba su komowa banza.


Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita, Sarakunan Mediyawa, da masu mulkinsu, da shugabanninsu, Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.


Ku sanar wa al'ummai da wannan, Su yi shirin yaƙi, Su kira mayaƙa! Su tattaro sojoji, su zo!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ