Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.
Za su zama kamar ƙarfafan mutane cikin yaƙi, Za su tattaka maƙiyi a cikin taɓon tituna. Za su yi yaƙi, gama Ubangiji yana tare da su, Za su kunyatar da sojojin doki.
Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba.
“Ga shi, ina gāba da ke. Ni Ubangiji Allah Mai Runduna na faɗa. Zan ƙone karusanki, Takobi kuwa zai karkashe sagarun zakokinki, Zan hana miki ganima a duniya. Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunki ba.”
ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”
Akwai takobi a kan mahayan dawakanta, da a kan karusanta, Da a kan sojojin da ta yi ijara da su Don su zama kamar mata, Akwai takobi a kan dukan dukiyarta domin a washe ta.