Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 51:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Bisa ga umarninsa ruwan da yake samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 51:16
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.


Amma Ubangiji ya aika da iska mai ƙarfi a tekun, hadirin ya tsananta ƙwarai har jirgin yana bakin farfashewa.


Sa'an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama, Aka ji muryar Maɗaukaki. Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.


A sa'ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro. Yunusa ya ji kamar zai suma saboda zafin rana da take bugun kansa. Sai ya so ya mutu, ya ce, “Gara in mutu da ina zaune da rai.”


Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ina yi da ku daidai yadda nake yi da Habashawa. Na fito da Filistiyawa daga Kaftor, Suriyawa kuwa daga Kir, Daidai yadda na fito da ku daga Masar.


Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da yake can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa'ad da yake magana.


Sa'an nan yakan ba da umarni, Ƙanƙara kuwa ta narke, Yakan aiko da iska, ruwa kuwa yakan gudu.


Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa, Sai ya tsere, Sa'ad da ya ji ka daka tsawa, Sai ya sheƙa a guje.


Sa'an nan sai ya sa iskar gabas ta hura, Da ikonsa kuma ya sa iskar kudu ta tashi.


Shi wanda ya hau cikin sararin sama, Daɗaɗɗen sararin sama! Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!


An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza, Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.


Kana da ƙarfi kamar na Allah? Kana iya tsawa da murya kamar tasa?


“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara? Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?


Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya, Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.


Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.


Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.


Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.


Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ