Irmiya 50:29 - Littafi Mai Tsarki29 “Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 “Ku kira ’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.