Irmiya 50:17 - Littafi Mai Tsarki17 “Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 “Isra’ila garke ne da ya watse da zakoki suka kora. Na farkon da ya cinye shi sarkin Assuriya ne; na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansa Nebukadnezzar sarkin Babilon ne.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’