Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 50:14 - Littafi Mai Tsarki

14 “Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, ku kewaye Babila, Ku harbe ta, kada ku rage kibanku, Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 “Ku ja dāgā kewaye da Babilon, dukanku waɗanda kuke jan baka. Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi, gama ta yi zunubi ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 50:14
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila.


Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka, Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka, Saboda jinin mutanen da ka zubar, Da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.


Saboda ka washe al'umman duniya da yawa, Sauran mutanen duniya duka za su washe ka, Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.


Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi. Amonsu yana kama da rurin teku, Suna shirya don yin yaƙi da ke, ya Babila.


Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe daga arewa Su faɗa wa Babila da yaƙi. Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su cinye ta. Kibansu kamar na gwanayen mayaƙa ne Waɗanda ba su komowa banza.


Duk waɗanda suka same su, sun cinye su. Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifi ba,’ Gama sun yi wa Ubangiji laifi, wanda yake tushen gaskiya, Ubangiji wanda kakanninsu suka dogara gare shi.


A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”


Ku ta da tuta a duniya, Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho, Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita, Ku kirawo mulkokin Ararat, da na Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita. Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai shugabanci yaƙin da za a yi da ita, Ku kawo dawakai kamar fāra.


Zan aika da masu casawa zuwa Babila, za su casa ta, Su bar ƙasarta kango. Za su kewaye ta a kowane sashi A wannan ranar masifa.


“Saboda kuna murna, kuna farin ciki, Ku da kuka washe gādona, Saboda kuma kuna tsalle kamar karsana a cikin ciyawa, Kuna haniniya kamar ingarmu,


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan karya bakan Elam, inda ƙarfinta yake.


Ku haura, ku dawakai, Ku yi sukuwar hauka, ku karusai! Bari sojoji su fito, Mutanen Habasha da Fut masu riƙon garkuwoyi, Da mutanen Lud, waɗanda suka iya riƙon baka.


Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.


Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.


Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa, Na kuwa aikata mugunta a gare ka. Daidai ne shari'ar da ka yi mini, Daidai ne ka hukunta ni.


Da Yowab ya ga an ja masa dāgar yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu Isra'ilawa, ya sa su gabza da Suriyawa.


Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.


Irmiya ya ce, “Na karɓi saƙo daga wurin Ubangiji. An aiki jakada a cikin al'ummai cewa, ‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gāba da ita, Ku tasar mata da yaƙi!’


Kada ku bar maharbi ya yi harbi da bakansa, Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa, Kada ku rage samarinta, Ku hallaka dukan sojojinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ