Irmiya 5:29 - Littafi Mai Tsarki29 “Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”