“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ Sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”
“Ku yi shela a cikin Yahuza, Ku ta da murya a Urushalima, ku ce, ‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’ Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce, ‘Ku tattaru, mu shiga birane masu garu.’