Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.
Abin da maƙiyana ke faɗa, Ba abin da za a yarda da shi ba ne, Su dai, so suke su hallakar kawai, Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake, Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.
Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi, Motsinsu kamar ƙugin teku ne. Suna haye a kan dawakai, A jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi Gāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”