Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 5:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Saboda haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Domin sun hurta wannan magana, Ga shi, zan sa maganata a bakinka ta zama wuta, Waɗannan mutane kuwa su zama itace, Wutar za ta cinye su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 5:14
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa.


Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini, “Ga shi, na sa maganata a bakinka.


Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu, Na karkashe su da maganar bakina. Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.


Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”


Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ