Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.
Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.
Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.
Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.
Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.’ ”