Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 49:32 - Littafi Mai Tsarki

32 “Za a washe raƙumansu da garkunan shanunsu ganima, Zan watsar da masu yin kwaskwas ko'ina, Zan kuma kawo musu masifu daga kowace fuska, Ni Ubangiji na faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Za a washe raƙumansu, garkunansu mai girma za su zama ganima. Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,” in ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 49:32
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”


Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.


Zan sa iska ta hura a kan Elam daga kusurwoyi huɗu na samaniya. Za ta watsar da mutane ko'ina, Har ba ƙasar da za a rasa mutumin Elam a ciki.


Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.


“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.


Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa'ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ