Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 49:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Ku tashi ku fāɗa wa al'ummar da take zama lami lafiya, Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare, Suna zama su kaɗai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 “Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi wadda take zama da ƙarfin hali,” in ji Ubangiji, “al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare; mutanenta suna zama su kaɗai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 49:31
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,


Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.


“Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya. Kin ɗauka kina da girma kamar Allah, Har kina ganin ba wani kamarki. Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba, Ko ki sha hasarar 'ya'yanki.


Da haka Isra'ila yana zaune lafiya, Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗai A ƙasa mai hatsi da ruwan inabi, Wurin da raɓa take zubowa daga sama.


Gama daga kan duwatsu na gan su, Daga bisa kan tuddai na hange su, Jama'a ce wadda take zaune ita kaɗai, Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al'ummai.


Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.


Ni Ubangiji na ce, “Ko da yake suna da ƙarfi, suna kuma da yawa, Za a datse su, su ƙare. Ko da yake na wahalar da kai, Ba zan ƙara wahalar da kai ba.


Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.


“A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”


“Tun daga ƙuruciya Mowab tana zama lami lafiya, Hankali kwance, Ba a jujjuya ta daga tulu zuwa tulu ba, Ba a taɓa kai ta bauta ba, Domin haka daɗin ɗanɗanonta bai rabu da ita ba, Ƙanshinta kuma bai sāke ba.”


Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.


Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.


Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a, Azzalumai masu girmankai sun raina mu!


Haka mugaye suke. Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.


Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah, Bari mutanen Kedar su yabe shi! Bari su da suke zaune a birnin Sela Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ