27 Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu, Za ta kuwa cinye fādodin Ben-hadad.”
27 “Zan cinna wa katangar Damaskus wuta; za tă ci kagaran Ben-Hadad.”
Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya.
Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.
Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.
Mai girmankai za ta yi tuntuɓe ta fāɗi, Ba kuwa wanda zai tashe ta, Zan ƙone garuruwanta da wuta, Zan kuma hallaka dukan abin da yake kewaye da ita.