Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 49:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu, “Hamat da Arfad sun gigice, Domin sun ji mugun labari, sun narke saboda yawan damuwa, Ba za su iya natsuwa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Game da Damaskus. “Hamat da Arfad sun giggice, gama sun ji mummunar labari. Suna damuwa, sun damu kamar tekun da baya hutu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 49:23
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu.


Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne?


Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.”


Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu.


Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama kufai! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa! Kwankwaso yana ciwo, Fuskoki duka sun kwantsare!


Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”


Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.


Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?”


A Dimashƙu gwamnan da yake ƙarƙashin sarki Aretis ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni,


Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.


ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.


Ku je ku duba a birnin Kalne. Sa'an nan ku zarce zuwa babban birnin Hamat, Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku?


Ina sarakunan biranen Hamat da Arfad, da Sefarwayim, da Hena, da Iwwa?”


Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.


A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.


Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,


Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama'ar Isra'ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta.


Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu.


Wannan zai sa jarumi wanda yake da zuciya kamar ta zaki ya karaya don tsoro, gama dukan mutanen Isra'ila sun sani tsohonka jarumi ne, su kuma waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.


Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,


Amma 'yan'uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama'ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci.


Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa.


“Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.’


Sarakunan Edom suka tsorata, Shugabannin Mowab suna rawar jiki, Dukan mazaunan Kan'ana sun narke.


Ashe, kogin Abana da na Farfar, wato kogunan Dimashƙu, ba su fi dukan ruwayen Isra'ila ba? Da ban yi wanka a cikinsu na tsarkaka ba?” Ya juya, ya yi tafiyarsa da fushi.


Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.


Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba?


Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.


Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ