Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 49:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da suke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 49:18
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hazor za ta zama kufai har abada, wurin zaman diloli, Ba wanda zai zauna a ciki, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”


Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.


Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, Na rantse cewa, Mowab za ta zama kamar Saduma, Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata. Za su zama ƙasar ƙayayuwa Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada. Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”


“Na hallakar da waɗansunku Kamar yadda na hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sanda kuke, wanda aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku komo wurina ba.


Abin da ya faru da Saduma da Gwamrata, Da biranen da suke kewaye da su, Shi ne zai faru da Babila. Ba mutumin da zai zauna cikinta.


Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.


da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,


Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta.


Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.


Kamar yadda Ishaya ya yi faɗa cewa, “Da ba domin Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba, Da mun zama kamar Saduma, An kuma maishe mu kamar Gwamrata.”


Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”


“Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato 'ya'yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ