Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 48:45 - Littafi Mai Tsarki

45 “A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yan gudun hijira suna tsaye ba ƙarfi. Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon, Harshen wuta kuma ya fito daga Sihon, Ta ƙone goshin Mowab da ƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

45 “A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 48:45
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.


Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta, A wannan birni na Heshbon, Sun cinye Ar ta Mowab, Ta murƙushe tuddan Arnon.


Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’


Daga cikinsu za a sami mafificin dutsen gini, Daga cikinsu kuma za a sami turken alfarwa, Daga cikinsu za a sami bakan yaƙi, Daga cikinsu kuma kowane mai mulki zai fito.


Zan aukar da wuta a ƙasar Mowab, Ta ƙone kagarar Keriyot. Jama'ar Mowab za su mutu a hargitsin yaƙi, Sa'ad da sojoji suke sowa, ana busa ƙahoni.


Gama Heshbon ita ce birnin Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.


Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,


Kaitonku, ku mutanen Mowab! Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace! Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira, Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.


Aka karkashe samari a cikin yaƙi, 'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.


Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan, Da dukan sarakunan Kan'ana.


Mutanen Memfis kuma da na Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.


Darajar Mowab ta ƙare. Ana shirya mata maƙarƙashiya a Heshbon, ‘Bari mu je mu ɓata ta daga zaman al'umma!’ Ke kuma Madmen za ki yi shiru, Takobi zai runtume ki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ