43 Tsoro, da rami, da tarko suna jiranku, Ya mazaunan Mowab, Ni Ubangiji na faɗa.
43 Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji.
Tsoro, da wushefe, Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.
Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
Ga shi, zan kawo muku razana daga waɗanda suke kewaye da ku, Za a kore ku, kowane mutum zai kama gabansa, Ba wanda zai tattara 'yan gudun hijira. Ni Ubangiji Allah Mai Runduna na faɗa.
Na kafa miki tarko, ya kuwa kama ki, ya Babila, Ke kuwa ba ki sani ba. An same ki, an kama, Domin kin yi gāba da ni.”