Darajar Mowab ta ƙare. Ana shirya mata maƙarƙashiya a Heshbon, ‘Bari mu je mu ɓata ta daga zaman al'umma!’ Ke kuma Madmen za ki yi shiru, Takobi zai runtume ki.
Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.
Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.
“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.
Gama ina tare da kai don in cece ka, Zan hallaka dukan al'ummai sarai, Inda na warwatsa ku. Amma ku ba zan hallaka ku ba, Zan hore ku da adalci, Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba hukunci, Ni Ubangiji na faɗa.”
Yanzu Ubangiji ya ce, “A shekara uku daidai, dukiyar Mowab mai yawan nan za ta ƙare. Daga cikin ɗumbun mutanenta 'yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”