Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 48:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Za a ci Keriyot a kuma kame kagarai. A wannan rana zukatan jarumawan Mowab za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 48:41
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.


Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.


Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”


Yanzu ku tambaya, ku ji, Namiji ya taɓa haihuwa? To, me ya sa nake ganin kowane namiji yana riƙe da kwankwaso, Kamar mace mai naƙuda, Fuskar kowa kuma ta yi yaushi?


Mutanen Urushalima sun ce, “Mun ji labarin yaƙin, Hannuwanmu suka yi rauni. Azaba ta kama mu, Ciwo irin na mai naƙuda.


Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.


Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata, An sa wa wuraren zamanta wuta, An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.


Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.


Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi, Ta juya, ta gudu, Tsoro ya kama ta, Azaba da baƙin ciki sun kama ta kamar na naƙuda.


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”


da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.


Akwai takobi a kan mahayan dawakanta, da a kan karusanta, Da a kan sojojin da ta yi ijara da su Don su zama kamar mata, Akwai takobi a kan dukan dukiyarta domin a washe ta.


Zan aukar da wuta a ƙasar Mowab, Ta ƙone kagarar Keriyot. Jama'ar Mowab za su mutu a hargitsin yaƙi, Sa'ad da sojoji suke sowa, ana busa ƙahoni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ