Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 48:40 - Littafi Mai Tsarki

40 “Ni Ubangiji na ce, Wani zai yi firiya da sauri kamar gaggafa, Zai shimfiɗa fikafikansa a kan Mowab.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 48:40
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.” Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar.


Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,


Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”


Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki, Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji, Domin mutanena sun ta da alkawarina, Sun kuma keta dokokina.


Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.


“Dawakansu sun fi damisa sauri, Sun fi kyarketan maraice zafin hali, Sojojin dawakansu suna zuwa a guje. Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa, Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.


Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri. Sun fafare mu a kan duwatsu, Suna fakonmu a cikin jeji.


Duba, ga abokin gāba yana zuwa kamar gizagizai, Karusan yaƙinsa suna kama da guguwa, Dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaitonmu, mun shiga uku!


Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ