“Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe.
Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.
Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.