Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra'ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata.,
Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.
Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”