Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab, “Kaiton Nebo, gama ta lalace! An kunyatar da Kiriyatayim, an ci ta da yaƙi, An kunyatar da kagararta, an rushe ta.
A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,