Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 48:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Ku da kuke zaune a Dibon, Ku sauka daga wurin zamanku mai daraja, Ku zauna a busasshiyar ƙasa, Gama mai hallaka Mowab ya zo ya yi gab da ku. Ya riga ya rushe kagararku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 48:18
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!


Amma yanzu an hallaka zuriyarsu, Tun daga Heshbon har zuwa Dibon, Har da Nofa kusa da Medeba.”


Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.


da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon,


Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,


Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.


Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”


daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,


suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon,


Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”


Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ