Irmiya 48:17 - Littafi Mai Tsarki17 “Ku yi makoki dominta, ku da kuke kewaye da ita, Dukanku da kuka san sunanta, ku ce, ‘Ƙaƙa sandan sarauta mai iko Da sanda mai daraja ya karye?’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gonakin da suke kusa da Heshbon, da gonakin inabin da suke Sibma an lalatar da su, gonakin inabin nan waɗanda ruwan inabinsu suke sa masu mulkin al'ummai su bugu. Da kurangunsu sun taɓa yaɗuwa zuwa gabas har suka kai birnin Yazar da cikin hamada, wajen yamma kuma sai da suka dangana da gefen Tekun Gishiri.