Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al'umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can.
Ubangiji ya ce, “Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi. Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.
Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da yake kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”
Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.