Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 48:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab, “Kaiton Nebo, gama ta lalace! An kunyatar da Kiriyatayim, an ci ta da yaƙi, An kunyatar da kagararta, an rushe ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 48:1
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon,


ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza.


da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”


ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.


Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama'ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki.


“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.


Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo.


Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.


Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau.


da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,


A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,


Allah zai lalatar da kagaran Mowab da dogayen garukansu, ya rushe su ƙasa su zama ƙura.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ