Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 47:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka huta? Sai ka koma ƙubenka, Ka huta, ka yi shiru!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 47:6
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.


Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”


“‘Ka mai da takobinka cikin kubensa. Zan hukunta ka a ƙasarka inda aka haife ka.


“Idan kuwa na jawo wa ƙasar takobi, na ce bari takobi ya ratse ƙasar, har na kashe mata mutum duk da dabba,


“Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’


Zan sa musu masu hallakarwa huɗu, in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar.


Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”


Har yaushe zan yi ta ganin tuta, In yi ta jin amon ƙaho?


Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”


Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su.


Ka zo, ya Ubangiji, Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su! Ka cece ni da takobinka daga mugaye,


Sa'an nan Ubangiji ya umarci mala'ikan, shi kuwa ya mai da takobinsa a kube.


Abner kuwa ya kira Yowab, ya ce, “Har abada ne takobi zai hallakar? Ba ka sani ba ƙarshen zai yi ɗaci? Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina runtumar 'yan'uwansu?”


Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!”


“La'ananne ne shi wanda yake yin aikin Ubangiji da ha'inci, La'ananne ne shi kuma wanda ya hana wa takobinsa jini.


Ni Ubangiji na ce, Akwai takobi a kan Kaldiyawa, Da a kan mazaunan Babila, Da a kan ma'aikatanta da masu hikimarta,


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ