Irmiya 46:9 - Littafi Mai Tsarki9 Ku haura, ku dawakai, Ku yi sukuwar hauka, ku karusai! Bari sojoji su fito, Mutanen Habasha da Fut masu riƙon garkuwoyi, Da mutanen Lud, waɗanda suka iya riƙon baka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.