Irmiya 46:27 - Littafi Mai Tsarki27 “Ya bawana Yakubu, kada ka ji tsoro, Kada ka firgita, ya Isra'ila. Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa da rai kwance, Ba wanda zai razanar da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202027 “Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila. Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa, zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance, babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |