Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza.
Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.