“Ifraimu horarriyar karsana ce, Wadda yake jin daɗin yin sussuka, Amma na sa wa kyakkyawan wuyanta karkiya, Na sa Yahuza ta ja garmar noma, Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya.
Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.
Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai Runduna ce, Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama wa maƙiyansa. Takobi zai ci, ya ƙoshi, Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna zai hallaka maƙiyansa, A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.
zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.