Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.
Gama daga kan duwatsu na gan su, Daga bisa kan tuddai na hange su, Jama'a ce wadda take zaune ita kaɗai, Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al'ummai.
Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi.