Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.
shi da yake yi mana ta'aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta'azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta'aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah.
daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,