Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 44:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa'adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.’ To, sai ku tabbatar da wa'adodinku, ku cika su!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 44:25
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.


Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.


“Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.


Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.


Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.


Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ