Irmiya 43:9 - Littafi Mai Tsarki9 “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da suke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da suke gaɓar Bahar Rum da waɗanda suke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da suke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.