Irmiya 43:12 - Littafi Mai Tsarki12 Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da suke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da suke gaɓar Bahar Rum da waɗanda suke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da suke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.