Irmiya 43:11 - Littafi Mai Tsarki11 Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da suke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da suke gaɓar Bahar Rum da waɗanda suke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da suke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.