Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 42:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Irmiya ya amsa ya ce, “Na ji ku, tabbatacce zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yadda kuka roƙa; zan faɗa muku duk abin da Ubangiji ya faɗa ba kuwa zan ɓoye muku kome ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 42:4
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba, Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe. Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka, Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.


Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu'a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwan da suke daidai.


Musa kuwa ya ce, “Nan da nan da tashina daga gabanka, zan yi addu'a ga Ubangiji, ƙudajen kuwa za su rabu da kai, da fādawanka, da jama'arka gobe, kada ka sāke yin ruɗi, ka ƙi barin jama'ar su tafi, su miƙa wa Ubangiji hadaya.”


Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanar da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida gida,


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto.


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.


Haka kowannenku zai ce wa maƙwabcinsa da ɗan'uwansa, ‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?’


“Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ