Irmiya 42:10 - Littafi Mai Tsarki10 ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.