Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 41:5 - Littafi Mai Tsarki

5 sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 sai ga mutane tamanin daga Shekem, Shilo da Samariya suka zo da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage, suka kawo hadayun gari da turare tare da su a gidan Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 41:5
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.


Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.


Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


“Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu.


Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki.


Abimelek, ɗan Yerubba'al, wato Gidiyon, ya tafi Shekem wurin dukan dangin mahaifiyarsa, ya ce musu,


Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.


Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.


A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra'ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra'ila a Samariya shekara ashirin da biyu.


Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel.


Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci.


domin haka zan yi wa Haikali wanda ake kira da sunana, wanda kuma kuka amince da shi, da kuma wurin da na ba ku, ku da kakanninku, kamar yadda na yi wa Shilo.


“ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila.


Bayinka suna ƙaunarta, Ko da yake an hallakar da ita, Suna jin tausayinta, Ko da yake ta zama kufai.


Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa'an nan suka sallame su.


Kasusuwan Yusufu, waɗanda jama'ar Isra'ila suka kawo daga Masar, an binne su a Shekem a yankin ƙasar da Yakubu ya saya a bakin azurfa ɗari daga wurin 'ya'yan Hamor mahaifin Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusufu.


sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.


Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,


Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.


Ya bar alfarwarsa da take a Shilo, Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.


Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.


Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani,


Baƙin ciki zalla ya sami Gaza, Ashkelon ta lalace. Ya ƙattin mutane, yaushe za ku daina tsattsage kanku?


Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.


Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci.


Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa'an nan ya sallame su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ