Dawuda bai bar mace ko namiji da rai ba, wato da zai kawo labari, a Gat, domin yana gudun kada su faɗi abin da yake yi, su ce, “Ga abin da Dawuda ya yi.” Abin da Dawuda ya yi ta yi ke nan a lokacin da yake zaune a ƙasar Filistiyawa.
sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.