Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 41:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Isma'ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da take tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutum goma waɗanda suke tare da shi suka kashe Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da takobi, suka kashe wannan da sarkin Babilon ya naɗa a matsayin gwamna a kan ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 41:2
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma a watan bakwai, sai Isma'ilu ɗan Netaniya, wato jikan Elishama, daga gidan sarauta, ya zo tare da mutum goma ya fāda wa Gedaliya, ya kashe shi tare da Yahudawa da Kaldiyawa da suke tare da shi a Mizfa.


Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi.


Sa'ad da shugabannin sojoji waɗanda suke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba,


Sukan sāka mini alheri da mugunta, Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.


Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.


Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel.


Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’


sai shugabannin, wato Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan da Jonatan, 'ya'yan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, da 'ya'yan Efai, mutumin Netofa, da Yazaniya ɗan mutumin Ma'aka suka tafi tare da mutanensu zuwa wurin Gedaliya a Mizfa.


Isma'ilu kuma ya kashe dukan Yahudawa da suke tare da Gedaliya a Mizfa da waɗansu sojojin Kaldiyawa da suke a wurin.


Suka ce masa, “Ko ka sani Ba'alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.


Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohenan ɗan Kareya, “Kada ka kuskura ka yi wannan abu, gama ƙarya ce kake yi wa Isma'ilu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ