Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 41:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 41:10
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka ce masa, “Ko ka sani Ba'alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.


Sa'ad da shugabannin sojoji waɗanda suke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba,


Amma sa'ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba'ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba'a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”


Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba'ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa'ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra'ila.


Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza.


Haka Ubangiji ya ce, “Rubuta wannan mutum, marar 'ya'ya. Mutumin da ba zai yi albarka a duk kwanakinsa ba. Gama ba wani daga zuriyarsa Da zai gāji gadon sarautar Dawuda, Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”


“Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ